Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Jihar Filato Sun Gamsu da Yadda Gwamnati Ke Biyansu a Kan Kari


Ranar Ma'aikata a jihar Filato
Ranar Ma'aikata a jihar Filato

Yayinda wasu ma'aikata ke korafi akan rashin biyansu albashi a kan lokaci su kuwa na jihar Filato yabawa gwamnatin jihar suka yi a yau ranar bikin ma'akata ta duniya

Ma'aikatan jihar Filato sun bayyana gamsuwarsu da tsare tsaren da gwamnatin jihar ta kirkiro na biyansu hakkokinsu akan lokaci.

A wani kasaitatcen taro da ma'aikatan suka gudanar domin tunawa da ranar ma'aikata ta duniya shugaban kungiyar ma'aikatan Kwamrade Jibrin Banchir yace gwamnatin jihar tana biyan ma'aikata albashinsu akan kari.

Yana mai cewa babu abun da zasu ce sai godiya ga Allah domin sun dade basu yi irin bikin na yau ba. Yace cikin shekaru biyu da zuwan wannan gwamnatin ana biyansu albashi da fansho a bisa kaida. A cewarsa bisa ga yin hankan an samu zaman lafiya a jihar.

Duk da cewa gwamnatin na biyan albashin a kan kari har yanzu akwai wasu kudaden da gwamnatin bata biya ba kamar mafi kankantan albashin matakin farko a kananan hukumomi da sauran kudin hutu da kuma kudin fanshon wadanda suka bar aiki kwana kwanan nan.

In ji Jibrin Banchir sun gane cewa ba fitina ba ce zata biya masu bukata. Irin shawarwari da su keyi da gwamnati ne zasu dinga kaisu samun nasara.

Sakataren 'yan fansho na jihar Bulus Ibrahim yace matsalolinsu sun ragu matuka in bar da batun kudin sallama.

Shi ma gwamnan jihar yace hakkinsu ne su kula da ma'aikatansu domin al'umma su samu yin walwala. Gwamna Lalong yace abun da suka ga shugaban kasa na yi ya kamata su yi. A cewarsa shugaban kasa yana farin cikin ya ga an biya ma'aikata akan lokaci. Yace biyan albashi ya kawo zaman lafiya.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG