Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan kare hakkin bil’adama a Najeriya sun koka


Wadansu masu zanga zanga
Wadansu masu zanga zanga

Ma’aikatan hukumar kare hakkin bil’adama ta Najeriya sun koka game da yadda suka ce shugabannin hukumar ke take musu hakkoki, lamarin da suka bayyana da cewa, na sanyaya musu gwiwa wajen kokarin bin diddigin masu kawo korafi ga hukumar domin a share musu jawaye,

Shekaru ashirin da suka shige ne aka kafa hukumar kare hakin bil’adama ta Najeriya, domin bin diddigin duk wani haki da aka tauyewa dan Najeriya ta kowacce fuska da suka hada da biyan albashi da kuma wadansu hakkokinsu.

To sai aka wayi gari suma ma’aikatan wannan hukuma, sun sami kansu a bangaren wadanda suke kokarin karewa, domin kuwa sun shafe watanni biyu ba a biya su albashi ba. Mai Magana da yawun ma’aikatan ya bayyana cewa, komi ya tabarbare a hukumar kare hakkin bil’adaman ta Najeriya, ya kuma zama abin takaici cewa, suna aikin kare hakkokin al’umma amma sub a a kare hakinsu ba.

Ya bayyana cewa, tilas ne su saurari masu kawo koke koke duk da yake babu kayan aiki a ofis din ba a kuma biyansu albashi.

Ma’aikatan hukumar sun yi kira ga ‘yan majalisa da gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike a kuma kawar da duk wadanda suke danne hakkin ma’aikatan.

Baya ga batutuwan da suka shafi batun albashi da kuma hakkokin aiki, ma’aikatan sun kuma koka kan yadda shugabanni suka hana su kafa kungiya da zata rika bin batutuwan da suka shafi sha’anin aiki da jin dadinsu.

Yajin Ma'aikatan kare hakkin bil'adama-2:56"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Ga cikakken rahoto da Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana daga Kano

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG