Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Na Nazarin Alamuran Kasar Sudan


Shugaban Sudan Omar al-Bashir da Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan ta hagunsa.

Duk da umurnin da shugaban kasar Sudan ya bayar na cewa a saki duk fursinonin siyasa da ake tsare dasu, ofishin jakadancin Amurka dake Khartoum ya ce har yanzu bata canza zani ba

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace tana nazarin al’amura a kasar Sudan bayan shugaban kasar Omar Al Bashir ya bada umarnin nan take a sako dukkan fursunonin siyasa daga gidan yari.

Kamfanin dilancin labarun Sudan da ake kira SUNA a takaice ne ya bada labarin umarnin sako fursunonin. To amma wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya fadawa Muryar Amurka cewa ya zuwa tsakar ranar jiya Talata goma ga wannan wata na Afrilu, babu wani tabbaci da aka samu na sako fursunonin.

Ofishin jakadancin Amurka a birnin Khartoum yana tuntubar iyalan wadanda aka sakon, domin jin halin da ake ciki.

Kamfanin dilancin labarun Sudan ya bada labarin cewa, bada umarnin sako fursunonin wani bangare ne na yunkurin inganta sasantawa da samun zaman lafiya makoni bayan da gwamnatin kasar tayi ta kamen, fada kan mai uwa da wabi domin dakile zanga zangar kin jinin manufofin gwamnati.

Rahoton bai baiyana yawan fursunonin da aka bada umarnin a sako ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG