Ministan shari'a kuma Antoni Janar ta Amurka Loretta Lynch, ta fada jiya Litinin cewa, ma'aikatar shari'a zata binciki rundunar 'Yansanda dake birnin Chicago, domin gano ko rundunar sannu a hankali tana keta tsarin mulki ta wajen amfani da karfin tsiya kan mutane.
Wannan matakin ya biyo bayan sakin wani fefen bidiyo watan jiya, wanda ya nuna yadda wani jami'in 'Yansanda ya harbe ya kashe wani matashi bakar fata dan shekaru 17 da haifuwa. Lamarin ya auku ne cikin watan Oktoban bara.