Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatar Sufurin Najeriya Ta Kaddamar da Shirin Gina Tasoshin Manyan Motoci


Ministan Sufuri Rotimi Amaechi a wurin kaddamar da tasoshin

A wurin kaddamar da shirin gina tasoshin manyan motoci a Abuja Farfesa Wole Shoyinka ya bukaci a soma jaraba direbobi kafin a barsu suna daukan fasinjoji

Farfesa Wole Shoyinka ya ce ya zama wajibi a dinga yiwa direbobi gwaji kafin a barsu suna daukan fasinjoji domin gano ko suna cikin hayacin tuka mota.

Wasu direbobin sukan kwankwadi giya, wasu kuma barci bai wadace su ba amma sai su hau hanya da motocinsu da sau tari akan gamu da munanan hadura.

Farfesa Wole Shoyinka wanda ya bada kasida a taron
Farfesa Wole Shoyinka wanda ya bada kasida a taron

Yanzu dai za’a fara da kafa tasoshi tara a shirin.Wuraren da za’a kafa tasoshin kuwa sun hada da garin Ogbulafor a jihar Enugu da Lokoja a jihar Kogi da Mararrabar Jos a Kaduna da kuma Illela a jihar Sokoto.

Shugaban kungiyar direbobin Najeriya Najim Usman Yasin ya ce suna maraba da tasoshin domin hakan zai taimaka masu suna saurarawa. Yace wurare taran da aka zaba wurare ne da motoci ke tsayawa.

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi na kan gaba wajen goyon bayan gina tasoshin. Ya ce babbar dabara ce aka kirkiro saboda kungiyar direbobin jiharsa ta fada masa cewa cikin watanni shida ta taba hasarar motoci wajen hamsin da daya da kaya saboda rashin wuraren tsayawa. Yana ganin tasoshin zasu taimaka wurin bunkasa tattalin arziki

Sashen tashar jiragen ruwa ke da alhakin gina tasoshin. A cewar shugaban hukumar jiragen ruwan kusan kashi casa’in na kayan masarufi dake shigowa Najeriya ana rabasu ne ta yin anfani da manyan motoci.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG