Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madagali: ‘Yan Gudun Hijira Sama Da 3000 Sun Koma Gidajensu


Ziyarar Tawagar Karamar Hukumar Madagali Sansanin Runduna Ta 143

‘Yan gudun hijira sama da 3000 sun koma muhallansu a karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa, sakamakon nasarar da rundunar soja ke samu na dakile hare-haren kunar bakin wake da na sari ka noke.

A wata hira da sashen Hausa ya yi da shugaban karamar hukumar Madagali, Alhaji Mohammed Yusuf, lokacin wata zirayar da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar suka kai sansanin soja a Madagali don jinjinawa da baiwa dakarun kwarin gwiwa.

Gwamnan jihar Adamawa, Muhammadu Umaru Jibrilla Bindo, wanda ya ce “yabon gwani ya zamo dole,” ya bukaci mazauna yankin su ja hakulan ‘yan uwansu dake zaman hijira da su koma gidajensu da yake yanzu zaman lafiya ya samu a yankin.

Kwamandan rundunar ta 143 dake da sansani a Madagali, Kanal Chidi Nlemadin, ya shaidawa tawagar cewa rufe kasuwar garin da rundunar ta yi, ta wucin gadi ce don kaucewa hare-haren kunar bakin wake da ake kaiwa watannin baya kan kasuwar. Ya ce rundunar ba zata jira har sai ‘yan ta’addar Boko Haram sun kai hari kafin su maida martini ba, ya ce suna bin su cikin daji suna fatattakarsu.

Wakilin Muryar Amurka, Sanusi Adamu, ya ziyarci yankin ya ce wata babbar matsala da yankin ke fama da ita, ita ce ta rashin hanyoyin sadarwa ta wayoyin salula, sakamakon lalata tasoshin sada sakonni da ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi shekaru uku da suka wuce.

Domin karin bayani saurari rahotan Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG