Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Janar Marwa a APC Sun Yi Gangamin Marabtar Shugaba Buhari a Jimeta


Gangamin marabtar shugaba Buhari a Jimeta

Magoya bayan Janar Buba Marwa a jami'iyyar APC sun yi gangamin marabtar shugaba Muhammad Buhari a Jimeta jihar Adamawa.

Duban jama'a masu biyayya ga Janar Buba Marwa karkashin inuwar jam'iyar APC ta jihar Adamawa sun yi jerin gwanon kan manyan titunan fadar jihar don nuna farin cikinsu da komowar shugaba Muhammad Buhari gida wasu 'yan sa'o'i da ya gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya.

Jagorar jerin gwanon masu yi wa shugaban\ Buhari fatar alheri, dan takarar gwamna a jihar a karkashi tutar rusashiyar jam'iyar NRC Alhaji Musa Bubakari Kamale ya fadawa taron cewa dawowar shugaban za ta samar da wata kafa ta murkushe ayyukan ta'addanci, sace sacen mutane, 'yan tsagerar Niger Delta da masu rubda ciki kan dukiyar al'umma da yanzu ke samun nasarori.

Da yake jawabi ga taron jama'a a bakin sabuwar kasuwar Jimeta, tsohon Dan majalisar dokoki na jihar Adamawa mai wakiltar karamar hukumar Yola ta arewa Hon. Hassan Turaki gugar zana ya yi ga wasu 'yan jam'iyyar APC a jihar da ba su da kyakkyawar fata ga shugaba Buhari wadanda ya ce tuni suka soma rabon mukamai lokacin da yake zaman jinya a Ingila.

Wata 'yar gani kashe in ta shugaba Buhari A'i Mai Ganda ta ce yayin da suke marhaba lale da dawowarsa ta ce akwai bukatar gwamnatin ta karkata hankalin ta wajen kyautatawa talakawa da masu fama da radadin matsin tattalin arziki.

Da yake fashin bakin jawabin shugaba Buhari, Alhaji Musa Bubakari Kamale ya ce matsayinsa kan masu kirar aware su gabatar da bukatarsu ga wakilan su dake majalisun tarayya wadanda ke hurumin tattaunawa kan makomar Najeriya ya gamsar da shi.

Sai dai gangamin ya tada batutuwa masu sarkakiya kan makomar jam"iyar APC mai mulkin jiha da ke fama da rarrabuwan kawuna inda kowane bangare ke da uban gida.

Saurari karin a rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG