Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Jonathan da Buhari Suna Bayyana Dalilan Cancantar a Zabesu


Buhari da Jonathan.

Yayin da 'yan takaran shugaban kasa na manyan jam'iyyu ke kara karkarewa da kemfen, magoya bayansu suna bayyana dalilan cantantarsu

Mataimakin kakakin daraktan kemfen din Jonathan Isa Mafindi yace yana da mahimmanci a sake zabar PDP ta cigaba da abun da ya kira ayyukan raya kasa.

Yace kowace shiyar kasar nada nata bukatun. Sabili da haka za'a zauna a shirya yadda za'a fitar da arziki daga shiyar ba wai sai an nemo kudin man fetur ba.

Amma a nashi bangaren Sanata Danjuma Goje na ganin zaban APC a duk matakan zabe shi ne zai zama abu mafi a'ala ga kasar. Idan an zabi Buhari amma 'yan majalisun tarayya da gwamnoni duk 'yan hamayya ne to Buharin ba zai iya yin aiki ba. 'Yan hamayyan ko su cireshi ko kuma su hana ruwa gudu. Ba zai iya kawo gyare-gyaren da ya kamata ya yiba.

Hukumar zabe zata fara zaben ne da na shugaban kasa daga ranar 14 ta watan gobe.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG