Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Shugaba Buhari Na Kiransa Ya Yiwa Gwamnatinsa Garambawul


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Har yanzu magoya bayan Shugaban Najeriya Muhammad Buhai na ganin wadanda suke kewaye dashi basa bin akidarsa saboda haka abun da ya fi shi ne ya yiwa gwamnatinsa garambawul

Har yanzu magoya bayan shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, na ci gaba da kiransa ya yiwa gwamnatinsa garambawul don ya samu cika alkawurran da ya dauka wa ‘yan kasar.

Haliru Sani Maiwa, jigo a “Kungiyar Abokan Buhari” ya nuna jin takaicin ganin har yanzu ‘yan PDP ne suka cika gwamnatin ta Buhari, suna rike da mukamai kuma shugaban yaki ya fitar dasu. A ganinsa, su ne suke yiwa gwamnatin Buharin zagon kasa.

Shima Ya’u Ciroman Bakan Daura, wani dan “ga ni kashe ni” na shugaba Buhari ya fada cewa shugaban kadai ne yake aiki amma duk sauran da suka kewayeshi basa taimaka masa.

A nashi gefen, Abdullahi Jalo, kakakin Kwamitin Riko na jam’iyyar PDP, yace har yanzu ayyukan da gwamnatinsu ta PDP tayi ne ake dogaro a kansu, babu wani sabon aiki da gwamnatin yanzu zata nuna da cewa nata ne.

Sai dai babban sakataren APC na kasa Mai Mala Boni yace gwamnatin Buhari ta gina tubalin duk wata nasara ga Najeriya kuma ya bada tabbacin cewa duk alkawurran da shugaban ya yiwa Najeriya zai cika.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG