Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaifin Jarumi Ibrahim Maishunku Ya Rasu


Ibrahim Maishunku, (hagu) Da Mahaifinsa, (Dama) - Hoto: Instagram Adam A. Zango
Ibrahim Maishunku, (hagu) Da Mahaifinsa, (Dama) - Hoto: Instagram Adam A. Zango

Mahaifin jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood Ibrahim Maishunku ya rasu.

Ya rasu ne a jiya Talata.

“Inna lillahi wa’inna Ilaihirraji’un. A yau 26 ga watan Janairu 2021, na yi babban rashi. Allah ya yi maka afuwa Baba.” Maishunku ya rubuta a shafinsa na Instagram.

Ya kara da cewa, “Wallahi duk wanda ya tafi cikin aminci ya huta. Allah ya ba mu hakurin rashinka Baba. Allah ya sa mu mutu cikin aminci.”

Tuni dai jarumai da furodusoshi da sauran masu ruwa da tsaki a masana'antar ta Kannywood suka yi ta mika sakon ta’aziyyarsu ga jarumin wanda ya yi suna da fim dinsa na “Madadi” da “Jamila Da Jamilu.”

“Allah ya jikan shi da rahama.” In ji Ali Nuhu.

"Muna rokon Allah ya jikansa da rahama @maishunku. Allah ya ba ka hakuri da juriya." Adam A. Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram.

“Allahu Akbar.” Halima Atete ta rubuta a sashen yin tsokaci na shafin Maishunku.

“Allah ya ji kan sa da rahama.” In ji Nazifi Asnanic.

“Allah ya jikan sa, yai masa rahama Ibraheem,” Falalu Dorayi ya ce.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG