Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahajjata 87 Ne Suka Rasa Rayukansu


Hukumomi a Saudiyya sun ce akalla mutane 87 ne suka halaka wasu 187 kuma suka sami raunuka lokacin da wata na'urar gine gine shigen kugiya ta burma kan harami a Makka.

Faduwar kugiyar ta bar baraguzai ta ko ina. Ana aikin fadada haramin ne lokacindahadarin ya auku.
Hotuna da ake nunawa a dandalin sadarwa sun nuna mahajjata jina-jina, da kuma baraguzai daga na'urar ginin da kuma banagaren masallacin da ya burma.
Wannan hadari ya auku ne lokacin da mahajjata daga sassan duniya daban daban suka hallara domin fara aikin hajji cikin wannan wata.

XS
SM
MD
LG