Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar-Mahajjata 78 Turereniyar Jifan Shedan Ta Halaka A Saudiyya.


Gawarwakin wasu mahajjata da turereniyar Muna ta halaka.

Kwamitin da gwamnatin kasar ta kafa ya mika rahotonsa wanda ya kunshi wadannan sabbin alkaluma.

A jamhuriyar nijer yayinda aka cika makwanni ukku da faruwar turereniyar Muna wadda ta hallaka daruruwan alhazai, kwamitin dake bin diddigin wannan al’amari domin tantance alhazan Nijer da abin ya rutsa da su ya bada rahoton bincikensa.

A yayin wani taro da manema labarai da suka kira a yammacin Jumma’a wakilan kwamitin da ke bin diddigin abubuwan da suka biyo bayan turmitsitsin na ranar jifan shaidan, suka tabbatar da cewa ya zuwa yanzu alhazai ‘yan nijer 78 ne suka rasu. Ali Umaru shine shugaban kwamitin.

Ali Umaru ya kara da cewa yanzu haka ba a san inda alhazai 41 ‘yan Nijer suka shiga yayinda aka kyasta 34 da suka ji rauni. Daga cikin wadanda suka rasu 48 ne kawai aka yiwa takardun rejistar mamata.

Kwamitin ya karyatar jita jitar cewa cikin rami guda aka bunne gawarwakin mutanen da suka rasu a turereniyar ta Muna. Kafin a kara samun wasu bayanan na daban a nan gaba, Shugaban kwamitin bin diddigi halin da alhazan Nijer suka shiga a yayin wannan iftila’i Ali Umaru ya bukaci jama’a su kara hakuri domin a cewarsa hukumomin Saudiyya na ci gaba da tantance ragowar gawawakin alhazai ta hanyar binciken zanen yatsu dan ganin an gano zahirin sunayensu da kasashen da suka fito.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG