Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahamat Deby Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa A Chadi


(Tsohon hoto) Shugaba Mahatam Deby Itno a N'Djamena a ranar Mayu 4, 2024.
(Tsohon hoto) Shugaba Mahatam Deby Itno a N'Djamena a ranar Mayu 4, 2024.

Alkaluman zaben sun nuna cewa Deby Itno ya samu kashi 61 cikin 100 na kuri’un da aka kada, yayin da Masra ya samu kashi 18.5.

Hukumar zabe a Chadi ta ayyana Shugaban mulkin sojin kasar Mahata Deby Itno a matsayin wanda ya lashe shugaban kasar da aka yi a ranar Litinin.

Sai dai babban abokin hamayyarsa, Firaiminista Succes Masra na kalubalantar sakamakon, wanda aka fitar a ranar Alhamis a matsayi na wucin gadi.

An dai fitar da sakamakon zaben mako guda gabanin wa’adin da aka yi tsammanin za a sanar da shi.

Alkaluman zaben sun nuna cewa Deby Itno ya samu kashi 61 cikin 100 na kuri’un da aka kada, yayin da Masra ya samu kashi 18.5 cikin 100.

Tun gabanin sakin sakamakon Masra ya yi zargin cewa an tafka magudi.

Zaben na Chadi ya wakana ne bayan shekaru uku da kasar ta zauna karkashin mulkin soji.

Tun da farko dama masu fashin baki sun yi hasashen cewa Shugaba Deby Itno ne ake sa ran zai lashe zaben wanda ‘yan takara goma suka fafata ciki har da mace daya.

A shekarar 2021 Shugaba Itno ya karbi raganar mulkin kasar daga hannun mahaifinsa da aka kashe a fagen daga, wanda ya kwashe shekru sama da 30 yana mulki.

Hukumar zaben kasar ta ce mutum miliyan 8.2 ne aka yi rijista don kada kuri’arsu a wannan zabe wanda aka tura dakarun kasar sama da dubu 26 su kare rumfunan zabe.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG