Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaukaciyar Guguwa Mai Ruwan Sama Ta Earl Ta Ratsa Ta Tsibiran Puerto Rico da British Virgin Islands


Hoton mahaukaciyar guguwa ta Earl tun lokacin da ta fara kankama a kan teku daga tauraron dan Adam

Jami'ai sun ce wannan mahaukaciyar guguwa tana tafe da iska mai juyawar kilomita 215 cikin awa daya, kuma zata yi barazana ga tsawon yankin gabashin Amurka

Mazauna tsibiran Puerto Rico da Virgin Islands (bangaren Britaniya) sun fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma iska mai dan karen karfi a yayin da mahaukaciyar guguwar nan ta Earl mai karfi ta ratsa ta arewacin tsibiran.

Jami'ai sun yi gargadin cewa wannan guguwa da hadari zasu juye ruwan saman da zai haddasa mummunar ambaliya da gocewar kasa daga tuddai.

Cibiyar Nazarin Mahaukciyar Guguwa ta Amurka dake birnin Miami a Jihar Florida, ta ce Earl tana tafe da iska mai juyawar kilomita 215 cikin awa daya, a wani lokacin kuma tana karuwa ta zarce haka sosai.

Masana kimiyyar yanayi sun yi hasashen cewa mutanen dake tsiviran Turks da Caicos za su ga ruwan sama mai tsananin yawa nan da gobe laraba.

Har ila yau an gargadi mazauna kudancin tsibiran Bahamas da su zauna cikin tsammanin ruwan sama mai tsananin yawa.

Masana sun yi hasashen cewa wannan mahaukaciyar guguwa ta ruwan sama za ta wuce ta gabas da tsibiran dake cikin tekun Carribean, kuma nan gaba cikin wannan makon zata yi barazana ga jihohin da suek gabashin nan Amurka.

A Antigua, ruwa ya malale yankunan da suek cikin kwari a kasar a yayin da guguwa mai tsanani a St. martin mai makwabtaka da nan ta tuge bishiyoyi ta kuma kwantar da sanduna da wayoyin lantarki.

Wannan mahaukaciyar guguwa ta sanya jiragen ruwan yawon shakatawa sun karkata jiragensu daga tasoshin da guguwar zata bi, yayin da jiragen sama a fadin yankin suka soke sauka ko tashin jiragensu.

XS
SM
MD
LG