Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahimmancin Makewayi Wajen Kare Jama'a Daga Cututtuca


Har yanzu akwai gidaje masu dama a biranai da kauyuka, a Najeriya da basu da ingantattun ba-haya ko makewayi

Ranar 19, ga watan Nuwamba na kowace shekara rana ce da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta ware domin fadakar da alumar duniya mahimmacin dakunan ba-haya da nufin taimakawa wajen kawarda cututtuca masu yaduwa dangi Cholera.

Sai dai kuma har yanzu akwai gidaje masu dama a biranai da kauyuka, a Najeriya, da basu da ingantattun ba-haya ko makewayi.

A kasashen duniya daban daban masamman wadanda suka ci gaba ba-haya wuri ne da ake dauka da mahimmacin wanda ake samarwa a wurare daban daban domin biyan bukatun jama’a .

Bayan wannan kuma makewayi na taimakawa wajen riga kafin yaduwar cututtuka da ake samu ta iska masamman Cholera da danginsa.

Toh Sai dai ganin yadda hukumomi da jama’a a Najeriya, ke ta samun matsala wajen tsaftar muhalli wasu ‘yan kasar na ganin cewa akwai bukatar dawowa da aiyukan duba gari a kasar da nufin tabbatar da tsafta tsakanin al’uma.

Wata kididdiga da kungiyar WTO mai kula da tabbatar da ingantattun gidajen ba-haya da kuma wayar da kan al’uma game da mahimmancin ba-haya ta fitar na cewa daga cikin kananan yara 5, akalla 1, na mutuwa kafin cika shekaru 5, a duniya a dalillin kamuwa da cututtucan da ake yadawa a sakamakon rashin tsaftar makewayi kuma masamman a kasashe masu tasowa irin su Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:01 0:00

XS
SM
MD
LG