Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahukuntan Nijar sun zargi 'yan adawa da yin kemfen ma Hamma Ahmadou


Tambarin Jamhuriyar Nijar

Mahukuntan Nijar suna zargin 'yan adawa da yiwa Hamma Ahmadou duk da ikirarin cewa sun dauki shawarar kauracewa zaben

Ranar 20 ga wannan watan za'a gudanar da zaben shugaban kasar Nijar zagaye na biyu amma mahukuntar kasar sun zargi 'yan adawa da yin farfaganda a wuraren da suke da karfi suna yiwa dan takararsu kemfen.

Inji mahukuntan kasar 'yan adawa na bin dare suna fadawa mutane su zabi Hamma Ahmadou.

To saidai kakakin jam'iyyar PNDS mai mulki reshen Kwanni yace janyewar 'yan adawan yaudara ce domin har gobe basu bar yin kemfen ba musamman inda suke ganin suna da karfi. Jam'iyyar PNDS tace su yaki zasu shiga na neman zabe babu ja da baya.

'Yan adawa sun yi fatali da zargin suna cewa masu mulki ne suka sauya salon yakin neman zabe suna bin dare suna kemfen inji Alhaji Isa Marai kakakin jam'iyyar MODEN Lumana.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG