Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahukuntan Poland Sun Bukaci Amurka Ta Kafa Sansanin Sojojinta A Kasarsu


Wasu sojojin Amurka dake kasar Poland a yanzu

A kokarin tsoratar da Rasha domin kada ta mamaye kasarsu, mahukumtan kasar Poland sun bukaci Amurka ta kafa sansanin sojojinta a kasarsu kamar yadda ministan tsaron kasar ya sanar

Kasar Poland ta bukaci jami’an Amurka da su kafa rundunar sojoji tare da zuba dubban dakarun Amurka, a wani mataki na tsorartar da Rasha.

A jiya Litinin, Ministan tsaron kasar, Marius Blaszczak, ya ce a kwanakin nan ya tattauna da hukumomin Washington kan yadda za a kafa matsugunin sojin Amurka na dindindin a kasar ta Poland.

“Wannan kasancewa ta dakarun Amurka a kasar, na da matukar muhimmanci wajen jefa tsoro a zukatan abokanan hamayya, Inji Minista Blaszczak yayin wata hira da ya yi da kafar Radio 1.

Kasar Poland ta jima tana nuna damuwa kan harkokin tsaro a yankin, tun bayan da Rasha ta mallake yankin Crimea daga Ukraine a shekara 2014.

A can birnin Moscow, Kakakin shugaban Rashan, Vladimir Putin, Dmitry Peskov, ya ce, tura karin dakarun yammaci a kusa da kan iyakokin Rasha, “ba zai kara komai ta fuskar tsaro da zaman lafiya a nahiyar ba.”

Facebook Forum

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG