Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Magana da Yawun Majalisar Wakilan Najeriya Ya Musanta Zargin da Aka Yiwa Kakakinta


 Hon Abdulrazak Sa'ad Namdas mai magana da yawun Majalisar Wakilan Najeriya first left
Hon Abdulrazak Sa'ad Namdas mai magana da yawun Majalisar Wakilan Najeriya first left

Wani lokaci can baya takaddama ta taso tsakanin magoya bayan kakakin majalisar wakilai da Oanarebul Abdulmummuni Jibril bisa zargin da ya yi na cewa kakakin majalisar Yakubu Dogara nada hannu a abun da ya faru da kasafin kudi

A taron manema labarai da Onarebul Abdulrazak Namdas ya kira ya musanta zargin da tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar ya yi akan kakakin majalisar.

Namdas ya bayyanawa Muryar Amurka abubuwan da ya fada. Yace duk wani zargi da Onarebul Abdulmummuni Jibrin ya yi akan kakakin majalisar da sauran shugabannin majalisar ba gaskiya ba ne. Yace duk abun da ya fada ba gaskiya ba ne.

Taron manema labarai na Hon Abdulrazak Sa'ad Namdas mai magana da yawun Majalisar Wakilan Najeriya first left
Taron manema labarai na Hon Abdulrazak Sa'ad Namdas mai magana da yawun Majalisar Wakilan Najeriya first left

Yace abun da shugaban kasa yake da niyar kashewa shi zai mikawa majalisa. Sai bayan majalisa ta zauna kai ta tantance, ta kara ko ta rage kasafin kuma shugaba ya sa hannu ya zama kasafin kudi a hukumance.

Yace lokacin da shi Abdulmummuni Jibrin ya yi shugabancin kwamitin kasafin kudi sun samu korafe korafe da yawa dalili ke nan da suka cireshi. Shi ne, wai, a lokacinsa baya aiki da sauran 'yan kwamitin sai ya boye yayi abun da ransa yake so.

Onarebul Namdas yace babu dan majalisa daya da ya fito yace abubuwan da Jibrin ke fada akwai gaskiya ciki. Yace zasu kai maganar gaban kwamitin majalisar a binciki abubuwan da yake fada domina san gaskiya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:23 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG