Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yayi Barna Mai Yawa A Yankin Ogoni


Hoton mai kwance kan ruwa a yankin Ogoni na NIger delta a kudancin Najeriya, kusa da wata matatar mai ta 'yan fasa kwabri, 24 Maris 2011

Majalisar Dinkin Duniya ta ce za a bukaci fiye da dala miliyan dubu daya domin wkashe man da ya tsiyaya cikin shekarun nan a yankin na kudancin Najeriya

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya yace yoyon mai na shekaru masu yawa a yankin Ogoni na kudancin Najeriya zai bukaci aikin kwashe mai mafi girma a duniya wanda kuma zai iya lashe kudi fiye da dala miliyan dubu daya.

Wannan rahoto, wanda Shirin Kula da Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya ya bayar yau alhamis, yace tsiyayar da danyen mai ya rika yi na tsawon shekaru hamsin a yankin, ta lalata ruwan sha a Niger Delta. Majalisar ta ce ruwan sha a wasu sassan yankin ya gurbace ta yadda sai an dauki matakin gaggawa a kai.

Majalisar ta shawarci gwamnatin Najeriya da kamfanonin mai da su kafa wani asusun farko na dala miliyan dubu daya domin aikin tsabtace dagwalon man wanda zai iya cin shekaru 30.

‘Yan raji sun ce tsiyayar mai ta lalata yankin al’ummar Ogoni, wadanda akasarinsu manoma ne da masunta.

Jiya laraba, kamfanin mai na Shell ya dauki alhakin kwararar mai da aka samu a 2008 da kuma 2009 a yankin Ogoni ya kuma yi alkawarin biyan diyya ga al’ummar Bodo wadanda suka kai karar kamfanin a kotu.

Ala tilas kamfanin Shell ya daina aiki a yankin Ogoni a shekarar 1993, amma har yanzu sauran bututu da kayayyakinsa dake can su na ci gaba da gurbata muhalli. Kamfanin yace gungu-gungun barayin mai sune suke haddasa kwararar man, hujjar da ‘yan raji suka yi watsi da ita. Kamfanin Shell yace yana kwashe duk man da ya tsiyaya, ko da ma barayin man ne suka haddasa ta wajen fasa bututu.

XS
SM
MD
LG