Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yiwuwa Shugaban ISIS Na Da Rai


Shugaban ISIS Abu Bakr al-Baghdadi
Shugaban ISIS Abu Bakr al-Baghdadi

Sabanin ikirarin kasar Rasha cewa ta yi nasarar hallaka al-Baghdadi, kungiyar ISIS ta fito da muryarsa wadda aka nada ya na maganganu kan wasu al'amuran kwanan nan ciki har da rigimar Amurka da Koriya Ta Arewa.

Jiya Alhamis kungiyar ISIS ta fitar da wata murya da aka nada wadda ta ce ta sako ne daga babban shugabanta Abu Bakr al-Baghdadi, wadda, muddun aka tabbatar, zai zama karon farko da jagoran 'yan ta'addan ya furta wani abu cikin kusan tsawon shekara guda.

Ba a san lokacin da aka dauki wannan muryar ba, koda yake an ji shi yana magana akan barazanar Koriya Ta Arewa ga Amurka da Japan, abinda ke nuna cewa mai yiwuwa kwanan nan aka nada.

Akasarin muryar mai tsawon minti 46, wadda kafar labarai ta Al-Furqan ta fitar, ayoyi ne da al-Baghdadi ke ja.

Idan aka tabbatar cewa muryar al-Baghdadi ce, hakan zai saba da ikirarin Rasha cewa wani harin da ta kai a watan Yuni a kusa da birnin Raqqa na kasar Siriya ya hallaka jagoran ISIS din mai yawan buya.

Kodayake, dama, jami'an gwamnatin Amurka sun ce sun yi imanin cewa al-Baghdadi na da rai bayan ikirarin na Rasha na kashe shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG