Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MAIDUGURI: Gidauniyar Gwamnatin Tarayya Ta Ba Wasu Asibitoci Tallafi


Ana ceton wadanda bam ya rutsa dasu a Maiduguri
Ana ceton wadanda bam ya rutsa dasu a Maiduguri

Gidauniyar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa saboda tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita a arewacin kasar ta soma bada tallafi.

Gidauniyar ta bada tallafin nera miliyan 40 ga wasu asibitoci biyu dake birnin Maiduguri.

Tallafin da Farfasa Sunday Ochoche ya mikawa asibitocin yace sun bada ne saboda tallafawa mutanen da suka tagayyara da kuma wadanda suka samu raunuka lokacin rigingimun Boko Haram. Ya kara da cewa zasu cigaba da tallafawa mutanen.

Asibitocin da suka samu tallafin su ne asibitin kwararru ko Specialist Hospital da kuma asibitin koyaswa na Jami'ar Maiduguri ko MUTH.

Wadannan asibitocin su ne suka fi daukan nauyin mutane mafi yawa da rikicin Boko Haram ya rutsa dasu.

Kowane asibitin ya samu tallafin nera miliyan ashirin ne.

Farfasa Ochoche yace sun yi la'akari da irin dimbin aikin da asibitocin suka yi kuma suna kan yi ya sa suka zo domin su san yadda zasu taimaka masu.

Sun yi yarjejeniya da asibitocin kuma tallafin shi ne na farko domin su cigaba da taimakon wadanda rikicin Boko Haram ya shafa ba kowa da kowa ba ne.

Shugaban asibitin koyaswa na Jami'ar Maiduguri Dr. Abdulrahaman Tahir yace nera miliyan 20 ba zata yi masu komi ba domin sun kashe fiye da nera miliyan 100 ko.To saidai hakan ya fi babu.

Ga rahoton Haruna Dauda Biyu da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG