Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Amurka Ta Fasa Kada Kuri'a Akan Inshorar Lafiya


Paul Ryan
Paul Ryan

Karin kwana guda ba iya baiwa Shugaban kasa Donald Trump da Yan Majalisar Jam’iyyarsa ta Republican damar aiwatar da Babban burin da suka dade suna son aiwatarwa ba, wanda kuma zai zamo jigon aiyukan sabuwar gwamnatin.

A faduwar bazata da ta faru, ‘Yan jam’iyyar Republican sun fasa gudanar da zaben dokar Inshorar lafiya mai matukar muhimmanci gab da za’a fara zaben a majalisa a jiya Jumma’a sakamakon asarar kuri’u da suka yi a majalisar ta wakilai.

Fasa kada kuri’ar ya zo bayan hayaniyar da ta faru ranar Alhamis yayin da shugaban majalisa ya daga kada kuri’ar da tunanin awanni ashirin da hudu zasu basu damar yin nasarar sokewa da kuma maye gurbin Inshorar tsohon Shugaban Kasa Barack Obama mai suna Affordable Care Act.

Kakakin majalisa Poul Ryan ya tattara tsirarun ‘Yan jam’iyyar Republican domin tattaunawar gaggawa a can kuryar Majalisar bayan ya baiwa shugaban kasa Donald Trump Labarin mara dadi a White House.

Shugaban kasa Donald Trump ya dora laifin faduwar sabuwar Inshorar akan Yan Jam’iyyar Democrats sakamakon rashin samun kuri’a ko guda daya daga wajen su.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG