Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Bata Tsayar da Ranar Sake Gayyatar Magu Ba


Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Bayanda shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sake mika sunan Ibrahim Magu ga majalisar dattawa bisa ga wasikar da ya rubuta mata har yanzu bata tsayar da ranar sake gayyatarsa badomin ta tantanceshi ba

Inji Kwamred Shehu Sani majalisar dattawan bata sa ranar da zata gayyato shi Ibrahim Magu ba domin ya bayyana a gabanta a cigaba da sake tantanceshi.

Ahalinda ake ciki ma majalisar zata jira sai shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya dawo daga hutunsa na kwana goma da ya dauka domin majalisar ta tabbatar da gaskiyar wasikar..

Shehu Sani yace idan sun tabbatar wasikar daga wurin shugaba ta fito ko kuma da yawunsa aka rubutata majalisar zata duba batun Ibrahim Magun. Inji Shehu Sani irin wannan ba shi ne na farko ba. Kasafin kudin bara da shugaban kasa ya gabatar masu an saceshi an yi wasu canje-canje balantana wasika mai shafi daya. Saboda haka majalisar sai ta tabbatar wasikar daga wurin shugaban kasa ta fito.

Duk ranar da majalisar ta gayyaci Ibrahim Magu idan ya iya kare kansa daga zarge-zargen da aka yi masa sai a sake tunane.

Shi Shehu Sani ya kara da cewa akwai bukatar mai taimakawa shugaban kasa kan majalisar dattawa Ita Enang ya bada tabbaci akan wasikar.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG