Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka Na Tantance Mace Ta Farko Da Zata Shugabanci Hukumar CIA


Gina Haspel wadda ake tantancewa domin ta zama shugabar hukumar CIA

A karon farko a tarihin Amurka majalisar dattawan amurka na tantance mace, Gina Haspel, ta zama shugabar hukumar CIA

Ana saura kwanaki biyu majalisar dattawa ta fara sauraron shaida don tabbatarwa da darektar hukumar leken asiri ta CIA mai riko Gina Haspel, ta shugabanci hukumar, fadar shugaban Amurka ta White House ta kare Gina cewa ita ce mace da ta cancanci wannan mukami.

Haspel dai 'yar shekaru 61 da haifuwa wacce take shugabancin hukumar a matsayin riko, tayi-tayin janye sunanta daga tantancewa saboda ta riki wannan mukami na dindindin, sakamakon damuwar da ta biyo bayan samunta da hannu a cikin wasu matakan tsananta matakan neman bayanai daga hanun fursinoni musamman wadanda ake zargi da ta'addanci, amma a cewar jami’an gwamnati, shugaba Trump na bata kwarin gwiwa cewa tayi tsayin daka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG