Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka Zata Fara Tantance Ministocin Trump


Mitch McConnell, shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawan Amurka

Yau Talata majalisar dattijai zata fara tantance wasu daga cikin mutanen da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya zaba domin basu mukaman ministoci karkashin gwamnatinsa.

Ana saran za'a tanatance takwas daga cikin mutanen cikin wannan mako. Za'a fara ne da dan majalisar dattijai na jam'iyar Republican Jeff Session, wanda Trump ya dauka ya zama Atoni Janar kuma ministan shari'a.

Wasu 'yan jam'iyyar Republican sun ce lokacinda shugaba Obama ya kama aiki a 2009,an amince da mutane da ya zaba a zaman farko. Senata John Barrasso ya gayawa Muryar Amurka cewa, suna fata za'a sakawa kura anniyarta.

Amma 'yan Democrat suna korafin cewa da yawa daga cikin wadanda Trump ya zaba suna sanyin jiki wajen cike ko bada bayanai da ake bukata daga duk wadnda aka baiwa irin wadannan mukamai.

Da yake magana shima kan ministocin da ya zaba, shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump yace, yana da kwarin gwuiwa duk zasu sami amincewa.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG