Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya, Gwamnatin Borno Sun Gina Gidaje 300 a Ngwom


Daya daga cikin rukunin gidaje 300 Da Hukumar Raya Birane Ta Majalisar Dinkin Duniya Da Gwamnatin Borno Suka Gina
Daya daga cikin rukunin gidaje 300 Da Hukumar Raya Birane Ta Majalisar Dinkin Duniya Da Gwamnatin Borno Suka Gina

Hukumar raya birane ta Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Borno sun bude wasu rukunin gidaje 300 a kauyen Ngwom da ke karamar hukumar Mafa a jihar.

Kauyen Ngwom dai na da tazarar kilomita shida ne daga babban birnin Maiduguri, wadda hukumar raya birane ta Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar gwamnatin Borno suka ce sun kashe Dala Miliyan daya wajen sake gina rukunin gidajen da suka hada da makaranta da asibiti da kasuwa da kuma garejin mota.

A cewar shugaban hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya, Edward Kallon, mutanen kauyen sun fuskanci hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram har sau biyu, tun daga shekarar 2013 da kuma 2017.

Ya ce an yi kaca-kaca da kauyen inda aka lalata gine-ginen da ke cikin kauyen da kuma makarantar firaimare guda daya da ake da ita, da dakin shan magani da kuma wajen kasuwanci.

Sama da mutane 100 ne aka kashe a wani hari da kungiyar Boko Haram ta kai kauyen, kuma an tarwatsa magidanta fiye da 2,300 daga cikin gidaje 370 da ke kauyen.

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, ya yabawa hukumar raya birane bisa ayyukan da suka gudanar a kauyen na Ngwom.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG