Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce An Sauya Sakamakon Zaben Majalisar Dokokin Haiti


Zababben shugaban Haiti, Michel Martelly, yace kammalallen sakamakon zaben da ya ba jam'iyyarsa kujeru 3 tak a majalisar dokokin tarayya, ba na gaskiya ba ne, kuma da alamun gwamnati mai barin gado ta sauya sakamakon ne da gangan.

majalisar da kuma kasashe masu bayar da agaji sun bayyana tababar sahihancin sakamakon, bayan da aka ga yayi dabam da wanda aka bayar tun farko

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tababa game da sahihancin sakamakon zaben ‘yan majalisar dokoki na kasar Haiti, a daidai lokacin da kasar take shirin rantsar da sabuwar majalisar dokokinta.

Majalisar, tare da manyan kasashe masu bayarda agaji, cikinsu har da Amurka, sun nemi dalilin da ya sa gwamnatin Haiti ta sauya sakamakon farko da aka samu na zabubbukan kujeru 18 na majalisar a lokacin da ta bayyana kammalallen sakamako. Jam’iyyar Unity Party ta shugaba Rene Preval mai barin gado ita ce ta ci moriyar 16 daga cikin kujeru 18 da aka sauya sakamakonsu.

majalisar Dinkin Duniya ta ce sakamakon ya tado da damuwa sosai a kan halalcin yadda aka kidaya kuri’un. Jiya asabar wasu sanatoci su 12 sun zargi jam’iyyar Unity ta Mr. Preval da laifin sauya sakamakon, sun kuma yi kiran da a kafa wata hukuma mai zaman kanta domin ta bincika.

Kammalallen sakamakon da aka bayyana zai ba jam’iyyar Unity kujeru 46 daga cikin kujeru 99 na majalisar wakilai, da kuma kujeru 17 daga cikin 30 na majalisar dattijai.

Tsohon shahararren mawaki Michel Martelly ya lashe kujerar shugaban kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada lokacin zabe, amma kuma jam’iyyarsa ta Reypons Peysan ta samu kujeru kwaya uku tak a majalisun dokokin tarayya biyu. Mr. Martelly yace wannan sakamakon ba zai karbu ba, kuma ba shi ne abinda al’ummar kasar suka kada lokacin zabe ba.

Gobe litinin ake sa ran rantsar da sabbin ‘yan majalisar dokokin kasar.

XS
SM
MD
LG