Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Kira A Tsagaita Wuta A Aleppo


Ban Ki-moon, babban sakataren Majalisar Dikin Duniya

Yau Talata Majalisar Dinkin Duniya ko MDD tayi kiran da a gaggauta tsagaita bude bude wuta a birnin Aleppo na kasar Syria inda alamurra suke tabarbarewa sakamakon fadan da ake gwbzawa a wurin.


Kimanin mutane miliyan biyu ke rayuwa a wurin da babu ruwa da wutar lantarki inji MDD a yau Talata. A yayinda yan tawayen Syria ke kusawa cikin birnin Aleppo inda gwamnati ke da rinjaye, jami’an kiwon lafiya sun shaidawa tawagar MDD irin tsaka mai wuya da wannan birni mafi girma a Syria ke ciki

Dr. Zaher Shaloul na kungiyar likitocin Syria dake jihar Chicago a nan Amurka ya shaidawa jami’an MDD cewa kananan yara basu samun madara. Likitocin na fama da tsananin karancin magunguna, da rashin jini ga mabukata da sauransu, sa’annan babu abinci kuma babu iskar gas ta dafuwa..
Dr. Samer Attar da shi kuma ke aiki da kungiyar likitocin Syria a Chicago, ya nunawa jami’an hotunan kananan yara da aka yanke kafafunsu da kuma masu raunin kwakwalwa. Yace asibitin Aleppo tamkar yana cikin rami ne saboda an katangeshi da buhunan yashi don kareshi daga harin bama bamai. Yace a wani asibitin da yake aiki ana jinyar marasa lafiya ne a dakunan karkashin ginin, saboda gujewa hari a dakunan dake sama.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG