Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Shirya Tsagaita Wuta Tsakanin Dakarun Yamal da 'Yan Tawayen Houthi


Shugaban Kasar Yamal Abed Rabbo Mansour Hadi

A Yamal hukumomin kasar na kyautata zaton dakarun kasar da 'yan tawayen Houthi zasu amince da sabon shirin tsagaita wuta na wani dan lokaci

Hukumomin Yamal na sa ran dakarun kasar da ‘yan tawayen Houthi, za su amince da wani shirin tsagaita wuta na tsawon kwanaki bakwai, idan suka hadu a wani taro da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a Switzerland domin kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Shugaban kasar, Abd Rabu Mansour Hadi, ya aikewa da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wata wasika, inda ya bayyana yadda shirin tsagai wutan zai kankama, tare da fatan za a kara tsawaita shirin idan har ‘yan bangaren Houthin suka amince.

A ranar Litinin din da ta gabata ne, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin na Yamal, Isma’il Ould Sheikh Ahmed, ya ba da tabbacin cewa bangarorin biyu za su tsagaita wuta na dan wani lokaci, bayan da ya ayyana cewa dukkaninsu sun himmatu wajen ganin an samu maslaha kan rikicin, a wannan zama da za a fara a ranar 15 ga watan Disamba.

Ana dai sa ran, jami’an Majalisar Wakilan kasar dake goyon bayan tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh, suma za su halarci wannan zama.

Rikicin Yamal dai ya halaka akalla fararen hula dubu 2,500 a wannan shekara, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.

XS
SM
MD
LG