Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Da Kashe Sojojinta A Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya


Wasu sojoji a Janhuriyar Afrika Ta Tsakiya

Yayin da al'amura ke cigaba da tabarbarewa a Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya, duk kuwa da gudanar da zabe cikin nasara a watan Janairun da ya gabata, an hallaka wasu sojojin Majalisar Dinkin Duniya biyu, al'amarin da ya sa Majalisar ta dinkin duniya ta koka.

Da kakkausan lafazi Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da kisan wasu sojojin kiyaye zaman lafiya, 'yan asalin kasar Maroko su biyu, a Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya.

An kashe sojojin na kiyaye zaman lafiya ne yayin da su ke rakiya ga motocin dakon mai a tazarar kilomita 60 yamma da garin Obo, inda wani mahari ya harbe su sannan ya tsere cikin daji.

A wani bayanin da aka fitar yau Laraba, Kwamitin Sulhun ya ce, "hare-hare kan sojojin kiyaye zaman lafiya na iya zama wani babban laifin yaki," sannan Kwamitin ya kara da jaddada cewa "wadanda su ka kai harin za su fuskanci tuhuma."

Janhuriyar Afirka Ta Tsakiyar ta tsunduma cikin rudami tun a 2013, lokacin da wasu 'yan tawaye, wadanda akasarinsu Musulmi ne, su ka kwace iko a wannan kasa mai rinjayen Kirista, su ka hambare Shugaban kasa na lokacin, Francois Bozize.

A watan Disamba na waccan shekarar, Majalisar Dinkin Duniya ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya wajen 13,000 zuwa kasar saboda kare mutane da kuma wasu ayyukan tabbatar da zaman lafiya.

Jami'an saka ido kan yadda ake kiyaye takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba sun fadi a watan jiya cewa tashin hankali na wanzuwa duk da yake an gudanar da zabe ta hanyar dimokaradiyya kuma cikin nasara a watan Fabrairun da ya gabata. Da dama daga cikin yankunan kasar da ke lunguna sun kasa zama karkashin ikon gwamnati.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG