Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Gana Da Jama'a


Cikin gari a birnin Kano.
Cikin gari a birnin Kano.

Majalisar Jihar Kano ta fito da wani sabon shirin samar da isasshen ruwan sha wa al'ummar jihar.

A karo na farko, majalisar dokokin jihar Kano ta gana da al'ummar jihar domin shawo kan matsalar samun isashen ruwan sha.

Tun da aka kirkiro jihar, al'umma basu taba biyan gwamnati kudin ruwan da suke sha ba. A kudurin da majalisar ta fito da shi, kungiyoyi masu zaman kansu, yan kasuwa da ma wasu na iya shiga harkar samarda ruwa na sayarwa al'umma. Majalisar ta ce gwamnati kadai ba zata iya samar wa al'ummarta ruwa ba.

To amma wasu masana sun ce akwai kuskure a shirin domin ruwa ko ina yake malakar gwamnatin tararya ne kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasar. Kamata yayi majalisar ta fara da gwamnatin tararya domin samun hanyar cimma manufarta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG