Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Neja Ta Gayyaci Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Akan Yawan Sace Mutane


GWMNAN JIHAR NEJA Alhaji Abubakar Sani Bello

Biyo bayan yawan sace mutane da ake yi a yankunan Sarkin Pawa da Pandogari, yankunan dake kan iyaka da jihar Kaduna ya sa majalisar dokokin Neja gayyatar kwamishanan 'yan sandan jihar domin neman masalaha

A jihar Neja, majalisar dokoki ta gayyaci kwamishanan 'yan sandan jihar ya bayyana gabanta ya bayyana mata matakan da yake dauka domin kawo karshen sace sace da kashe kashen mutane da ake yi a jihar musamman a yankuna biyu.

A cewar majalisar sace mutane domin neman kudin fansa na kara ta'azzara a jihar, musamman a yankunan Sarkin Pawa da Pandogari dake kan iyaka da jihar Kaduna. Lamarin na matukar tayar da hankalin majalisar.

Onarebul Sha'aibu Liman Iya shugaban kwamitin labarai na majalisar ya yiwa Muryar Amurka karin haske. Ya ce majalisa ta ga ya kyautu a gayyato kwamishanan 'yan sandan akan yawan sace sace da kashe kashen mutane a jihar. Lamarin tsaro ne da ya shafi kowa a jihar.

Kakakin 'yan sandan ASP Abubakar Dan Inna ya ce duk da cewa takardar gayyatar kwamishanan bata isa wurinsu ba amma suna da abun shaidawa majalisar akan sha'anin tsaron jihar.

A makon jiya rundunar 'yan sandan ta nunawa manema labarai wasu mutane 13 da ta zarga da kwarewa wajen yin garkuwa da mutane tare da yi masu kisan gilla.Cikin mutane akwai wani mai suna Lawal Kwali da aka ce shi ne shugaban muggan mutanen.

Lawal Kwalin ya shaidawa Muryar Amurka cewa ya yi laifin kashe mutane. Ya amince da kashe mutane 30.

Ranar Litinin mai zuwa ne kwamishanan zai bayyana gaban majalisar.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG