Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar dokokin Nijar ta amince a ciwo bashi domin inganta wutar lantarki a karkara


Jamhuriyar Nijar

A karkashin dokokin da majalisar ta amince dasu kimanin biliyan goma sha shida na kudaden sefa ne gwamnatin ta Nijar zata ranto daga bankin cigaban Afirka ta yamma domin inganta wutar lantarki a yankunan karkarar kasar

Onarebul Iro Sani mataimaki na farko na kakakin majalisar dokokin kasar yace dokokin biyu da suka amince dasu sun shafi ayyukan wutar lantarki da za'a yi a garuruwa dari biyu da goma sha daya.

Cikin garuruwan dari biyu da goma sha daya akwai wasu yankuna hamsin da biyar da suma zasu samu wuta daga garuruwan.

Kodayake 'yan adawa sun amince da shirin amma suna cewa ba girin-girin ba ta yi mai. Kakakin gungun 'yan majalisa masu adawa Onarebul Lamido Mummuni Haruna yace an bada shekaru biyu a maida kudin.Burinsu ne a ciwo bashi wuraren da za'a samu da sauki ba tare da wasu sharudda ba. Yace sun yadda a ciwo bashi a yiwa talakawa aiki amma ba wasu su wawure kudin ba aikin kuma ba'a yi ba.

Wani abu kuma da 'yan adawa suka nuna damuwa kai shi ne rashin saka yankin Diffa a tsarin. Yace Diffa tana cikin matsala bai kamata a cireta daga shirin ba.Yanzu ne Diffa ke bukatar wuta.

Amma a bangaren masu rinjaye lamarin ba haka yake ba. Sun ce akwai shiri na musamman da suka yiwa Diffa saboda garuruwan Diffa nada nisa. Yace sun sani tana cikin uzuri saboda haka shiri na daban za'a yi mata.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG