Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Kasar Nijar Ta Bukaci Hukumar Zabe Ta Cike Gurbin Hamma Ahmadu


Hamma Ahmadou, shugaban jam'iyyar MODEN Lumana wanda yake gudun hijira a kasar turai

Majalisar dokokin kasar Nijar ta bukaci hukumar zabe ta maye gurbn Hamma Ahmadu shugaban jam’iyyar MODEN Lumana wanda baya kasar kuma shekaru biyu ke nan bai taka majalisar ba. Da kuri’u takwas cikin goma sha daya ne kwamitin gu

Da kuri’u takwas cikin goma sha daya ne kwamitin gudanarwa na majalisar dokokin Nijar ya amince ya aikawa hukumar zaben kasar da ta aika da wanda zai maye gurbin dan majalisa Hamma Ahmadu bayan ya yi sama da shekara biyu bai taka majalisar ba.

Shi dai Hamma Ahmadu yana gudun hijira ne a Turai sanadiyar gujewa wata shari’ar da ake yi masa a kasar wadda yake ganin wata makarkashiya ce ta siyasa.

Duk da cewa kotun kasar bata yanke shawara akan bukatar majalisar dokokin kasa na maye gurbinsa, ‘yan adawa, musamman na kusa da shi Hamma Ahmadun, irinsu Bala Ibrahim ya dora laifin wannan al’amarin kan jam’iyyar PNDS mai mulkin kasar. Yace lokacin da Hamma Ahmadu ya bar kasar bashi da lafiya. Jam’iyya mai mulki na gani Hamma ne zai zama masu kaya a zaben 2021 idan Allah ya kai rai.

Kokarin Muryar Amurka na jin ta bakin ‘yan majalisar dokokin kasar ya cutura, amma mai magan da yawun jam’iyyar PNDS Adamu Manzo ya ce an umurceshi ya jira matsayin kotun tsarin mulki kafin ya yi magana.

Sai dai kakakin PNDS Alhaji Asumana Muhammadou ya mayar da martini akan bugun kirjin da jam’iyyar MODEN Lumana ta Hamma Ahmadu ke yin a cewa PNDS zata hadu dashi a zaben 2021. Yana tunashesu cewa a zaben da ya gabata shugaban kasa Issoufou Mahammadou ya lashe zaben da kashi 83 yayinda ya doke Hamma. A cewarsa Hamm aba zai basu tsoro ba.

Dangane da wanda zai tsayawa jam’iyyar MODEN Lumana a zaben 2021, ‘yan jam’iyyar sun ce babu kowa sai Hamma a cewar Bala Ibrahim saboda wai sun yadda dashi.

A saurari rahoton Souley Barma da karinbayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG