Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Kolin APC Ta Kira Taron Gaggawa Akan Furucin Aisha Alhassan


Sanata Aisha Jummai Alhassan Ministar Harkokin Mata dake goyon bayan Atiku Abubakar kan tsayawa zaben shugaban kasa a shekarar 2019
Sanata Aisha Jummai Alhassan Ministar Harkokin Mata dake goyon bayan Atiku Abubakar kan tsayawa zaben shugaban kasa a shekarar 2019

Majalisar kolin jam'iyyar APC ta kira taron gaggawa akan furucin Aisha Alhassan, ministar harkokin mata, da ta yi makon jiya tana cewa zata goyi bayan Atiku Abubakar idan ya fito takarar shugaban kasa koda Shugaba Buhari ya sake tsayawa.

Yayin da ake sa ran shugabanin jam’iyar APC a Najeriya zasu gudanar da wani taron gaggawa inda ake sa ran zasu tabo batun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da minstar harkokin mata Sanata Aisha Jummai Alhassan,tuni masana da kuma kungiyoyi suka soma maida martani.

Koda yake kawo yanzu uwar jam’iyar APC din ta kasa bata fito karara ta bayyana matakin da zata dauka kan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma ministar harkokin mata ba,to amma tuni wasu masana ilimin siyasa suka soma gargadi ga uwar jam’iyar da kada ta riga mallam massallaci.

Abdulmumini Ibrahim Song,malamin kimiyyar siyasa ne a kwalejin kimiyya da fasaha na jihar Adamawa,wanda ma ya taba zama dan majalisar dokoki,yace duk wani mataki ladabtarwa da jam’iyar ka iya dauka za’a yi masa kallo ta fuska biyu.

Ya zuwa yanzu kokarin ji daga bakin shugabanin jam’iyar ta kasa bai samu nasara ba saboda duk wadanda ya kamata su yi magana suna kukan Rashin samun lokaci.To sai dai kuma tuni kungiyoyin dake fafutukar kare muradun Atiku Abubakar suka soma tsokaci kan wannan batu.

Koma da menene dai yanzu lokaci ne kawai ke iya tabbatar da yadda wannan dambarwar zata kaya.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG