Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar wakilan Girka ta aince da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati


Yan sandan kwantar da tarzoma a kasar Girka.
Yan sandan kwantar da tarzoma a kasar Girka.

Domin samun taimakon kasashen duniya, Majalisar wakilan kasar Girka ta amince da wani shirin tsuke bakin aljihun gwamnati. Ita kasar ta Girka tana fama da matsalar basussuka.

Majalisar Wakilan Girka ta amince da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati a zaman mataki na farko, da nufin ganin kasashen duniya sun ceci wannan kasa, daga dimbin basussukan da suka yi mata katutu.

Jiya Laraba, Prime Ministan kasar, mai ra'ayin gurguzu, George Papandreou, ya samu amincewar shirinsa, daya tanadi kara harajin dala miliyan dudu 40, da rage kudin da gwamnati ke kashewa yi da kuma sayar da kadarorin gwamnati. An amincewa shirin da kuri’a 155 da 138 da ratar daya wuce yadda aka zata tunda farko.

Wakilan Majalisar sun kada kuri’ar amincewar ce a daidai lokacin da masu zanga-zangar da basu kaunar wannan shiri, wadanda suke jifa da duwatsu suka yi arangama da ‘yan sanda a rana ta biyu a kan titunan da ke kusa da ginin Majalisar wakilai da ke tsakiyar birnin Athens. ‘Yan sanda dai sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar, a yayinda hayaki ya turnuke dandalin da ke kusa da Majalisar.

Wasu masu zanga zangar sun bankawa ofishin gidan waya dake cikin ginin ma'aikatar kudi ta kasar wuta. Ko da kuwa asusun IMF da kungiyar kasashen turai sun baiwa kasar Girka dala biliyan goma sha bakwai, kasar tana da niyar neman karin taimako daga wasu kasashen duniya.

XS
SM
MD
LG