Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Za Ta Dawo Zama Kan Batun Aringizon Kasafin Kudin Bana


ABUJA: Hon Abdulrazak Sa'ad Namdas mai magana da yawun Majalisar Wakilan Najeriya first left
ABUJA: Hon Abdulrazak Sa'ad Namdas mai magana da yawun Majalisar Wakilan Najeriya first left

Majalisar Wakilan Najeriya zata dawo zama bayan hutun mako Takwas da duba batun Aringizo a kasafin Kudin Bana.

Sai dai babu mamaki Majalisar ta dauki mataki kan tsohon shugaban kasafin Kudi na Majalisar Abdulmumin Jibrin, wanda ya zargi shugabannin Majalisar da Aringizo a kasafin har ma yayi musu kiran da suyi murabus.

Tun fara takaddamar dai Majalisar ta tafi hutu da ake ganin da zarar ta dawo zama Talatar nan zata fara tattaunawa ne kan lamuran Aringizon.

Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya EFCC ta fara binciken zargin, wannan takaddama dai ta kawo ra’yoyin mabanbanta tsakanin masu ganin ‘yan Majalisar na da zargin da zasu amsa da kuma masu ganin sunyi aiki ne bisa ka’idarsu ta dokar aikin Majalisa.

Abin tambaya anan shine ko ‘yan Majalisar zasu amsa wannan kira, a zahiri dai babu bangaren da ya sassauta. An rawaito dai shugaban kwamitin Labarun Majalisar Wakilan Abdulrazak Namdas, na cewa Majalisar zata dau matakai ne bisa doka, don haka sai a jira zaman Majalisar don ganin irin matakin da za a dauka.

Domin karin bayani saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG