Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Najeriya

Majalisar Dokokin Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamiti Don Binciken Bashin El-Rufa’i


Tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai
Tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai

Da alamu dai sabanin da aka fara samu tsakanin gwamna Uba Sani na jahar Kaduna da tsohon gwamnan jahar Malam Nasiru Ahmed El-rufai na kara tsanani.

Wannan na zuwa ne biyo bayan bayyana damuwa kan bashin da gwamnan Uba Sanin ya ce ya gada. Jiya Talata Majalisar dokokin jahar Kaduna ta kaddamar da kwamiti don binciken bashin da tsohon gwamnan ya ciwo da kuma yadda aka yi da shi.

Wannan ne dai karon farko da Majalisar dokokin jahar Kaduna ta dauki dumi biyo bayan kudurin bin diddigin bashin da tsohon gwamnan Malam Nasiru Ahmed El-rufai ya ciwo a jahar Kaduna shugaban kwamitin bibiyar shiga da fitar kudin jahar Kaduna na Majalisar dokokin jahar Hon. Mugu Yusuf daga karamar hukumar Kaura ya yi.

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani

Hon. Henry Mara shine shugaban kwamatin yada labarai na majalisar dokokin jahar Kaduna kuma ya ce wajibi ne su yi wannan bincike saboda ayyukan da aka ce don su aka karbo bashin basu kammala ba.

Sai dai daya daga cikin magoya bayan tsohon gwamnan Hajiya Aisha Galadima da ta dawo daga hannun jami'an saboda sukar gwamnatin Malam Uba Sanin ta ce akwai sauran danbarwa.

Aisha Galadima ta ce duk abun da aka yi a gwamnatin Malam Nasiru El-rufai da gwamna Uba Sani aka yi saboda idan bincike ne har da shi za a yi.

Barista Mohammed Ibrahim Zaria na cikin masu sharhi a kadafen yada labaru kuma jigon jamiyyar APCn ne, ya ce ruwa ne kawai ya yi tsami tsakanin gwamna Uba Sani da tsohon gwamna El-rufai shi yasa aka kafa wannan kwamitin bincike.

Alakar siyasa tsakanin gwamna Uba Sani da tsohon gwamnan Malam Nasiru El-rufai dai ta kullu tun tsohowar gwamnatin Olusegun Obasanjo kuma ba a taba jin kansu ba sai yanzu abun ya sa wasu ke ganin rigima ce mai sarkakiyar da ka iya cinye kujerun masu mukaman siyasa da dama a jahar ta Kaduna.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG