Hedikwatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana manufofinta game da makamin nukiliya a shekarar 2018, wanda ya hada da inganta makamin na nukuliya da kuma sabunta makaman Amurka na yanzu, saboda ayi shakkar fara duk wani yakin nukiliya da Amurkar.
“Abin da mu ke kokarin yi shi ne mu tabbatar da cewa jami’an diflomasiyyarmu da wakilanmu a wurin tattaunawa na cikin yanayin da ya wajaba a saurare su a duk lokacin da mu ka tayar da batun tsai da wanzuwar makamai,” a cewar Ministan Tsaron Amurka Jim Mattis ga Manema labarai a gabanin fitar da wannan bayanin jiya Jumma’a.
Shugaban Amurka Donald Trump y ace ya umurci Mattis ya sake nazarin yanayin makamin nukiliyar ‘yan kwanaki bayan da ya fara aiki.
Facebook Forum