Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makokin Kashe 'Yar Rajin Kare Muhalli Berta Caceres Ta Kasar Honduras


Masu Zanga-Zanga Rike Da Zanen Hoton 'Yar Rajin Kare Muhalli Berta Caceres, Suna Allah Wadai Da Kasheta

Dubban masu zaman makoki a kasar Honduras, sun fito a yau Asabar bisa kashe wata mai fafutukar kare muhalli Berta Caceres.

Ita wannan mata na kan fafutukar tsayar da wani akin hakar Dam din ka iya zama hatsari ga al’umma ne kafin a kasheta. Magoya bayan ‘yar gwagwarmayar sun dauko akwatin gawarta daga gidan mahaifiyarta zuwa Coci.

Inda suna tafe suna rera take da ke cewa, “Berta Na Raye”, sannan tare da yin kira ga yi mata adalci akan kisan gillar da aka mata. A shekarar 2015 da ta gabata, Caceres dai ta samu lambar yabo game da kare muhalli da ake kira Goldman Environmental Prize.

An dai kashe wannan ‘yar talika ne a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai mata har gida. Harin da ake zargin an shirya shi ne musamman don hallaka ta. To amma an cafke akalla mutum daya bisa zargin alaka da kisa.

Tuni dai dama gwamantin Honduras ta sa ana tsaron lafiyarta saboda yawan barazanar da ake mata, duk da yake dai ta sha kukan jami’an tsaron nata na sakaci sosai.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG