Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makomar Yarjajjeniyar Nukiliya: Kerry Da Shugaban Iran Sun Caccaki Trump


John Kerry

Janye bayar da tabbaci da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, kan sahihancin salon kasar Iran na kiyaye yarjajjeniyar nukiliyar da aka cimma da ita a 2015, na dada gamuwa da suka daga masu ra'ayin yarjajjeniyar daga sassa daban-daban na duniya.

Tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry, yayi tir da shawarar da Shugaba Donald Trump ya yanke, ta kin tabbatar da cewa Iran na kiyaye yarjajjeniyar nukiliya, wadda da ita da manyan kasashen duniya shida su ka rattaba hannu a kai a 2015.

Kerry ya ce wannan shawarar, a ta bakinsa, “ta yi hannu riga da abin da ke tartibi, saboda kawai nuna isa da kuma cimma wata manufa.” Kerry, wanda shi ne ya wakilci Amurka wajen tattauna kan yarjajjeniyar, ya kara da cewa Trump “ya nakasa mu, ya nesanta mu daga abokan huldarmu, ya karfafa masu ra’ayin rikau a Iran, ya sa warware rikicinmu da Koriya Ta Arewa zai dada yin wuya, wanda zai kuma dada kaimu ga yaki.”

Shugaban Iran ya fadi ranar Jumma’a cewa yarjajjeniyar da kasarsa da manyan kasashen duniya shida su ka rattaba hannu akai a 2015, ba za ta warwaru ba.

A wani jawabin da aka yada ta gidan talabijin na kasa bayan kalaman na Trump, Shugaban na Iran Hassan Rouhani, ya yi kira ga dukkan bangarorin da su ka rattaba hannu kan yarjejjeniyar da su kiyaye ta. Ya bayyana yarjajjeniyar da wata mashahuriyar aba da aka taba cimma a matakin difflomasiyyar kasa da kasa.

Shugaban na Iran ya kuma mai da martani game da bayyana Iran da kasa mai bin tafarkin kama karya da Trump ya yi, ya na mai bayyana Shugaba Trump da makaryaci kuma dan kama karya.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG