Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta'addanci Da Kunar Bakin Wake Haramun-Malaman Islama A Afghanistan da Pakistan da Indonesia.


Shugaban Indonesia Joko Widodo, a wannan hoto tareda malaman addinin Islama daga Afghanistan, da Pakistan da Indonesia. A taron kan ta'addanci.

Malaman addinin Islama daga Afghanistan, da Pakistan,da Indonesia sun jaddada cewa hare haren kunar bakin wake a Afghanistan dama a yankin baki daya haramun ne kuma ya sabawa manufofin addinin islama.

Malaman addinin Islama daga Afghanistan, da Pakistan,da Indonesia, sun jaddada cewa hare haren kunar bakin wake a Afghanistan dama a yankin baki daya- haramun ne kuma ya sabawa manufofin addinin islama. Malaman sun bayyana hakan a dai dai lokacinda suka hallara domin taron wuni-daya a Bagor a Indonesia, da zummar tattaunawa kan tarzomar da take ci a Afghanistan.

Taron da aka yi ranar Jumma'a,yazo ne watanni bayan da malaman Pakistan su fiyeda dubu daya da dari takwas, suka yi fatawar da take Allah wadai da ta'addanci ta ko wace fuska a kasar.

Afghanistan, ta soki fatwar ta Pakistan, domin ta yi Allah wadai ne ga ta'addanci a Pakistan kadai. Taron da ake yi a Bogor, an hada harda malaman Pakaistan ne, domin ana ganin suna da tasiri kan kungiyoyin mayakan sakai dake Pakistan.

Ahalinda ake ciki kuma,'Yansanda a Indonesia sun ce, 'yan kunar bakin wake sun kai hari kan majami'u ukua a birnin Surabaya dake tsibirin Java. Jami'ai suka ce akalla mutane biyu sun mutu, wasu 13 suka jikkata.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG