Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaysia Ta Mika Takardan Kuka Ga Makwabciyarta Singapore Kan Kalaman Batunci Da Bayanan Sirrin Amurka Suka Danganta Ga Jami'an Singapore


Wutar daji a Indonesia,sai dai wutar difilomasiyya ce take neman kama kasar da makwabciyarta Singapore,kan fallasarar bayanan difilomasiyyar Amurka.

Malaysia ta mika takardar kuka a hukumance ga Jakadan Singapore dake Kuala Lumpur, kan kalamai marasa dadi da kungiyar WikiLeaks ta bayyana,cikin takardun sirrin Amurka.Yau

Malaysia ta mika takardar kuka a hukumance ga jakadan Singapore dake Kuala Lumpur, kan kalamai marasa dadi da kungiyar WikiLeaks ta bayyana,cikin takardun sirrin Amurka.

Yau Talata,ma’aikatar harkokin wajen Malaysia ta fidda sanarwa inda ta bayyana “matukar rashin jin dadinta” kan kalaman, cikin takardar da ta mikawa jakadan Singapore. Ranar lahadi, wata jaridar Australia, ta buga bayanan sirrin difilomasiyyar Amurka, da ya nuna jami’an Singapore suna radar kasashe makwabta da batunci. Kasashen sun hada da Malaysia,Thailand,India,da kuma Japan.

An ambaci jami’an suna zargin “Yan siyasa da basu da kan gado” a Malaysia, da janyo wani “yanayi na rudani mai hadari” cikin kasar. Suna gargadin sai tayu Malaysia ta fuskanci fitinar kabilanci,da zai iya sanya ‘yan kasar China dake Malaysia, su shiga gudun hijira zuwa Singapore.

Jiya litinin, jami’an Singapore suka bayyana kwarin guiwar cewa dantakarsu da makwabtanta yana da karfin hana fallasar yi musu illa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG