Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Man. City Da Man. United: Wa Zai Mika Kai Bori Ya Hau?


Wata karawa da kungiyoyin suka yi a shekarar 2019.

A karo na 185, Manchester United za ta yi karawar hamayyar cikin gida da Manchester City a ranar Lahadi a gasar Premier League ta Ingila.

Dukkan kungiyoyin na saman teburin gasar inda yayin da Man City ke jan ragamar teburin da maki 65, Manchester United na biye da ita da maki 51 a gasar.

Idan dai Man City ta lashe wannan wasa, za ta kara fadada tazarar da ke tsakaninta da Manchester United da maki 17, akasin hakan kuma zai ba Manchester United damar rage yawan tazarar da ke tsakaninsu.

City ce dai za ta karbi bakuncin Man United a filin wasa na Etihad, wacce ta lashe wasanninta 20 da suka gabata, tun bayan da ta yi kunnen doki da West Bromwich Albion da ci 1-1 a ranar 15 ga watan Disambar bara.

Ba dai lallai ba ne Paul Pogba ya samu damar buga wannan wasa saboda raunin da ya ji a cinyarsa, amma ana ganin Victor Lindelof zai iya fara buga wasan yayin da kungiyar ke ci gaba da fuskantar matsalar masu tsaron gidanta.

Ita kuwa City a karon farko a wannan kakar wasa, ba ta da wani dan wasa da yake jinya tun bayan dawowar Nathan Ake.

Manchester United, kungiya ce da ta dogara da kwarewar ‘yan wasanta a matsayinsu na gashin kansu, siddabarun da wasu suke ganin bai cika dorewa ba.

Ita kuwa City ta shahara ne wajen kai samame ta kowanne sako idan ta hadu da abokanan hamayyarta.

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG