Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Da Chelsea Sun Sami Gurbin Gasar Zakarun Turai


Manchester United
Manchester United

Manchester United da Chelsea sun sami gurbin gasar Zakarun Turai a kakar wasanni mai zuwa, a yayin da Bournmouth da Watford sun fadi daga gasar ta Premier.

Kungiyoyin kwallon kafar Manchester United da Chelsea sun sami gurbi a gasar zakarun Turai ta kakar wasanni mai zuwa, bayan da duka kungiyoyin biyu suka yi nasara a wasanninsu na karshe na gasar Premier a ranar Lahadi.

Tun a makon jiya ne Liverpool ta daga kofin na gasar Premier ta bana da aka soma tun a ranar 19 ga watan Agustan bara, to sai dai kuma aka dan dakatar da ita na tsawon watanni 3 sakamakon annobar coronavirus.

United ta karkare a matsayin ta 3 teburin gasar ta Premier bayan da ta yi nasarar doke abokiyar takararta Leicester City da ci 2-0, a yayin da ita ko Chelsea ta karkare a matsayin ta 4, bayan da ita ma ta doke Wolves da ci 2-1.

Chelsea
Chelsea


Leicester da ta karkare a matsayin ta 5 tebur ko za ta fafata gasar Europa League a kakar wasanni mai zuwa, tare da Tottenham, wadda ta karkare a zaman ta 6, bayan da ta yi kunnen doki da Crystal Palace da ci 1-1.

A can kasan tebur kuma Bournmouth da Watford sun fadi daga gasar ta Premier kasancewar su a matsayin na 28 da 29 a kasan tebur, inda suka bi sahun Norwich wadda ta sami tabbacin faduwa daga gasar tun a makon da ya gabata.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG