Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maniyatta aikin hajjin bana daga jihar Niger sun yi zanga zangar


HAJJ 2016

Daruruwan maniyyata aikin hajjin bana daga jihar Niger sun gudanar da zanga zangar lumana domin nuna bacin rai akan yadda suka ce sun share kwanaki suna zaune a sansanin Alhazai ba tare da an kwashe su zuwa kasa mai tsarki ba,

Daruruwan maniyyata aikin hajjin banadaga jihar Niger, arewa maso yammacin Nigeria sun gudanar da zanga zangar lumana domin nuna bacin rai akan yadda suka ce sun share kwanaki suna zaune a sansanin Alhazai ba tare da an yi jigilarsu zuwa kasa mi tsarki ba.

Maniyattan wadanda akasarinsu sun fito ne daga yankunan karkarar jihar, sun shedawa wakilin sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari cewa suna cikin wani yanayin na rashin sanin tabbas gameda tafiyar tasu. Wasu daga cikin su, sunce sun share sama da kwanaki goma a sansanin Alhazai ba tare da an baiyana musu matsayin su gamaeda da tafiyar ba.

To amma jami'ar watsa labarai a hukumar Alhazai, Malama Hassana Isa Wushishi ta baiyana dalilin samun jinkirin. Tace saboda lamuran tsaro dake jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria, shi yasa aka karkata ko kuma aka fi maida hankali wajen kwashe maniyatta aikin hajji daga yankin. Dalili ke nan da aka samu tsaiko a cewar Malama Hassana.

Kawo yanzu dai kusan dukkan manyan jami'an hukumar Alhazai sunyi batan dabo daga sansanin Alhazan. To amma shugaban kwamiti mai kula da harkokin aikin hajji a Majalisar wakilan jihar, Salihu Mohammed yace manyan jami'an hukumar sun boye ne, domin kada maniyattan da suka fusata su huce haushinsi akan jami'an

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG