Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan PDP Reshen Arewa Maso Yamma Sun Kaiwa Shugaba Jonathan Ziyarar Sada Zumunta


Tambarin jam'iyar PDP mai mulkin Najeriya

Tsohon ministan tsaron Najeriya Bello Halliru ne ya jagoranci tawagar

Bayan ziyarar da 'yan PDP reshen Sakkwato su ka kaiwa Bamanga Tukur a kwanakin baya, su ma masu ruwa da tsaki a jam'iyar PDP reshen arewa maso yammacin Najeriya sun kaiwa shugaba Goodluck Jonathan ziyarar mubaya'a a karkashin jagorancin tsohon ministan tsaro Bello Halliru, wanda ke tare da gwamnan jahar Kebbi Saidu Dakingari, da na Katsina Shehu Shema, da Ramalan Yaro na Kaduna da kuma mataimakin gwamnan Sakkwato Mukhtari Shagari. Sai dai a wannan tafiya ba a ga jiga-jigan jam'iyar ta PDP a yankin ba irin su gwamnan jahar Jigawa Alhaji Sule Lamido da kakakin Majalisar Wakilai Aminu Waziri Tambuwal. Daga cikin tawagar da ta gana da shugaba Goodluck Jonathan har da Shetiman Rijiya, Faruk Ahmed Gusau dan kwamitin shugabancin jam'iyar PDP a yankin na yammacin Najeriya wanda ya yiwa wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu el-Hikaya karin bayani a kan ziyarar da ya ce ta sada zumunta ce:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG