Kungiyar kwallon kafar Marseille ta kasar Faransa “ba ta sayarwa ba ce”, a cewar shugabanta Jacques-Henri Eyraud a yau Assabar, biyo bayan rahotannin cewa wasu hamshakan attajirai na yunkurin saye kungiyar.
Eyraud ya kara da cewa “mu na Godiya ga dukkan wadanda su ka nuna sha’awar sayen kungiyar, to amma ba mu da ra’ayin sayar da ita.”
Kalaman na Eyraud na zuwa ne baya rahotannin cewa hamshakin attajirin nan da a da ya ke mallakar kungiyar kwallon zari-ka-ruga ta Toulon ta kasar Faransa Moura Boudjellal, ya yi tayin sayen Marseille a kan kudi yuro miliyan 700, daidai da dalar Amurka miliyan 785, amma tare da hadin gwiwar masu saka jari na kasar Saudiyya.
Tayin ya kumshi yuro miliyan 300 na sayen kungiyar, miliyan 200 na biyan basuka da kuma wasu yuro 200 na sayen ‘yan wasa.
Kungiyar ta Marseille da ta lashe gasar zakarun Turai a shekarar 1993, ta na karkashin mallakar attajirin ba’amurke Frank McCourt tun daga shekarar 2016.
Facebook Forum