Accessibility links

Masanan kiwon lafiya sun bukaci a rika yiwa mata masu ciki gwajin cutar HIV domin hana yada kwayar cutar daga uwa zuwa ‘ya’ya.

Masanan kiwon lafiya sun bukaci a rika yiwa mata masu ciki gwajin cutar HIV domin hana yada kwayar cutar daga uwa zuwa ‘ya’ya. Daya daga cikin masu wannnan kiran, Dr Johnson Oyeniyi, yayi kira domin yin gwajin ainihi da bada shawara domin rage karuwar cutar kanjamau tsakanin uwa da yaronta a cikin mata masu juna biyu.

Oyeniyi yayi wannan kiran ne a lokacin taron wayar da kai na kwana uku kan cutar sida a Omu-Aran, babban birnin karamar hukumar Irepodun, a jihar Kwara wanda kungiyar hadin kai kan yaki da cutar sida ta jihar Kwara ta shirya tare da hadin kan kwamitin yaki da cutar na jihar.

Dr. Oyeniyi wanda shine darektan gudanarwa a jihar, yace ana bukatar yin kyakkyawan gwaji gwaji na ainihi da kuma bada shawara tagari da zasu taimaka da kare al’umma gaba daya daga kamuwa da cutar.

Yace dole kowanne kayan aiki da ake bukata ya zamana wajen kiyaye sabuwar kamuwar cutar sida tsakanin Uwa da ‘yaronta. Oyeniyi yace yaron jaririn da aka haifa ba tare da an yiwa uwarshi gwajin tantance ko tana dauke da kwayar cutar HIV ba, yana cikin hadarin kamuwa da cutar.

Bisa ga cewarshi, wadansu fannonin da ake fuskantar kalubala a kokarin yaki da cutar kanjamau sune rashin amfani da shawarwari da kuma kin kiyaye umarnin likitoci da kuma nuna halin ko in kula da mutane suke yi a kan batun kula da lafiyarsu.

Masanan sun tsayar da shawarar fadakar da maza musamman domin su rika barin matansu suje awo su kuma yi gwajin tantance ko suna dauke da kwayar cutar HIV.
XS
SM
MD
LG