Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masarautar Suleja ta Nisanta Kanta da Siyasa


Fulanin jihar Njea

Masarautar Suleja ta nisanta kanta daga shiga duk wasu alamura na siyasa a jihar Neja ko a tarayya.

Masarautar dake cikin jihar Neja ta kuma isanta kanta daga duk wata jam'iyyar siysa. Ta rungumi "'yan babu ruwanmu".

A wani taron manema labarai masarautar ta ce hankalinta ya tashin akan wasu kalamun batanci ga masarautar da wani dan siyasa ya rika bazawa. Tace lamarin baraza ne ga zaman lafiyar yankin.

Alhaji Yusuf Baba Dan Galadiman masarautar wanda kuma shi ne hakimin Kabula shi ya yi magana a madadin sarkin Suleja Malam Muhammad Lawal Ibrahim. Yace ita masarauta uwa ce ga kowa. Yace duk wata jam'iyya da gwamnati ta san da ita ashirye suke su karbeta domin a samu cigaban gari.. Ya kira jama'a da su bi jam'iyyar da suke so ba tare da wani tsangwama ba.

Musabbabin wannan kashedin shi ne kalamun batanci da wani dan siyasa ya keyi sanoda wai ya nemi wata sarauta a masarautar. Mutumin ya kuma zargi sarkin Suleja Mohammad Awal Ibrahim da yin magana da wasu manyan jihar.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG